Kamfanin tura da wutar lantarki na ƙasa TCN ya ce ƙarfin wutar da ake samarwar a ƙasar nan ya kai megawatt 5,420.30 a karon farko a tarihi.
Sanarwar hakan a ranar Alhamis ta ce an turar wutar mai ƙarfin megawat 5,42.30 ne a kan mizanin 50.10Hz daga ranar Talata 18 ga watan Agustan 2020.
“Wannan shi ne adadi mafi girma da aka taba samarwa a tarihinƙasar nan, wanda ya haura megawatta 5,377.50 da aka samu daga ranar 1 ga Agusta, 2020 a kan mizanin megawatt 42.50”, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na TCN Ndidi Mbah ya bayyana.
Sanarwar mai taken ‘An kafa tarihin ƙaruwar wutar lantarki zuwa megawatt 5,420’, ta alakanta samun daidaituwar wutar a Najeriya da yadda gwamnati ta mayar da hankali a kan ɓangaren.
https://dimokuradiyya.com.ng/majalisa-ta-dakatar-da-shirin-karin-wutar-lantarki-har-sai-2021/
Ta ce hakan ya faru sakamakon shirye-shiryen da gwamnatin ta ƙaddamar domin faɗaɗa ɓangaren lantarki da kuma yunƙurin masu ruwa da tsaki a kasuwancinsa.
TCN ta kuma bayyana aniyarta na yin aiki ba kama ƙafar yaro wajen ingantawa da kuma daidaitar wutar lantarki a faɗin Najeriya.
Ta ƙara da rokon ‘yan ƙasa da su ba ta haɗin kai ta hanyar bayar da kariya da kadarorinta da ke faɗin kasar nan baki ɗaya.