Kimanin mako guda kenan kawo yanzu da aka samu wata mummunar jaravawa ta kifewar jirgin ruwa a Jihar Kebbi, a yanzu haka hukumomi dun bayyana cewa an gani gawarwakin mutane 97.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Alhaji Sani Dododo wanda ta bakinsa aka ji wannan sanarwa a yammacin jiya Laraba yayin wani taron majalisar Zartaswar, ya kuma kara tabbatar da cewa an samu karin wasu mutane sama da ashirin da ransu.
Alhaji Dododo ya ce a yanzu haka majalisar ta cimma matsaya kan kafa wani kwamiti don binciko Musababbin aukuwar wannan hatsari da aniyar kiyaye gaba.
Har ila yau Dododo ya ce ana wani shiri kuma na tabbatar da wata doka da za ta tilasta bin Ka’idojin bin duk wata hanya ruwa a jihar, a wani mataki na dakile yawan hadduran jirgin ruwa.
Daga cikin dokokin kamar yadda ya bayyana akwai rage tafiye-tafiyen dare da hana yara masu kuruciya tuka jirgi hadi da lodi maras kima.
Daga cikin mutane 97 da aka gano, bakwai daga cikinsu yan jihar Zamfara ne.