Zanga-zangar Lumana a bakin ƙofar shigar Majalisar Dokokin Jahar Filato, ta ɗauki sabon yanayi, a yayinda ƙungiyoyin matasa guda biyu da suka jiɓanci Majalisar suka faɗama juna da faɗa.
Akwai matasan da suka jiɓanci Shugaban Majalisar Dokokin Jahar Abok Ayuba, suke ɗauke da takarda, an hange su suna rawa kusa da babbar ƙofar shiga gidan, amma da misalin ƙarfe 8:30 na safe, wasu matasa sun shiga farfajiyar Majalisar ta hanyar ƙofar dake bayan Majalisar.
Wasu daga cikin su, sun fashe gilasan ƙofofin da zasu kai mutum zauren Majalisar, a yayinda shugaban Majalisar da ake dambarwa a kanshi da wasu ƴan Majlisar dake mashi biyayya, suke cigaba da taro.

KARANTA WANNAN LABARIN: Fira Ministan Japan Kishida Ya Ayyana Samun Nasara Bayan Zabe Mai Tsauri Daya Gudana
A sa’ilinda matasan dake waje suka gane cewa akwai wasu matasa a cikin majalisar, wanda kuma sune masu biyayya ga Yakubu Sanda, suka nemi shiga majalisar ta hanyar ƙarfi.
Wannan lamari ne ya sanya jami’an tsaro suka fara harbe-harbe a saman iska, domin fasa taron matasan, amma wasu matasan sun kasance a ƙasa, wasu kuma suka ruga domin neman maɓuya, sun kuma dawo tare da waƙoƙin su, da bayyana takardun su.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, harbin bindiga da akeyi ya rage, amma matasan sunyi cincirindo a majalisar.