Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Gombe, ya bayyana cewa a cikin shekarar 2020 an samu hatsura 278 a jihar.
Kwamanda Ishaku Ibrahim ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin ganawarsa da manema labarai a garin Lafiyawo dake karamar hukumar Akko ta jihar. Inda ya ce hatsarin ya auku ne a tsakanin watan Janairun 2020 zuwa Disambar shekarar.
Ibrahim ya ce hatsarin ya rutsa da mutum 1, 576 inda ya ci rayukan mutum 66 ya kuma raunata 812 a yayin da mutum 698 suka tsira da rauni ko mutuwa.