Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum Talatin da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar.
NCDC tunda fari ta wallafa a shafinta na Twitter da misalin karfe 9:20 na daren ranar Talata 14 ga watan Afrilu cewa an sake samun karin mutum 19 da ke dauke da cutar.
Sannan da misalin karfe 11:00 na daren ranar NCDC, ta sake wallafa cewa an samu wasu karin mutum 11 da suka kamun, abin da ya kai adadin wadanda suka kamu a ranar 30.
Hukumar ta ce cikin wadanda suka kamu 25 a jihar Legas suke, sai 2 a Abuja da 1 a Kano sai 1 a Akwa Ibom da kuma 1 a Edo.
Ya zuwa hada wannan rahoton mutum 373 ne suke dauke da cutar a Nijeriya a yayin da 99 suka warke, 11 suka rasu.