Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana cewa duk da cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda na ci gaba da tattaunawa don neman kudin fansa ta hanyar amfani da wayar tarho, an samu gagarumar nasara tun lokacin da aka fara hada layikan waya da lambar dan kasa ta NIN.
Ministan wanda ya bayyana hakan a garin Umuahia na jihar Abia yayin bikin ranar tantancewa ta duniya, ya ce tun da aka fara kokarin aiwatar da wannan tsari an samu raguwar kiran da ‘yan damfara ke yi wa masu amfani da wayar da ba su ji ba gani.
KARANTA ANAN: Yajin Aikin ASUU: NANS Tayin Barazanar Rufe Filayen Jiragen SamaN Najeriya
Ya ce bai kamata mutane su yi tsammanin kirkire-kirkire za su kawar da sharri da aka kulla cikin cikin dare ba, yana mai cewa a hankali ake bi domin fatattakar hskan.
“Batun kiran masu garkuwa da mutane ya ragu sosai dangane da kudin fansa ta waya. Ba za a iya tsaftace tsarin ba, gaba daya, sai dai za a iya gyara shi a hankali.”
Bata garin da ake kira da 419 da muka saba samu a mafi yawan lokuta a zahiri sun ragu saboda yawancin lambobin a yanzu suna maƙale da NIN.
A don haka ne ya bukaci karin lokaci domin ci gaba da kawar da bata garin, wadanda ke ci gaba da haifar da tsaiko ga zaman lafiyan Najeriya.
A wani labarin kuma: Wani Dan China Ya Yi Ajalin Budurwarsa ‘Yar Najeriya Mai Shekaru 23 Da Haihuwa
Wani dan kasar China ya daba wa masoyiyarsa wuka, wata matashiya ‘yar shekara 23 a duniya a Janbulo, karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’ar nan bayan wanda ake zargin ya kawo wa marigayiyar ziyara, mai suna Ummakulsum Sani Buhari, a gidan iyayenta da ke kusa da ofishin hukumar kula da muhalli ta Kasa (NESREA).