By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar mutane uku ‘yan gida daya sakamakon wata gobara data tashi a garin Otukpo dake karamar hukumar Otukpo a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Sewuese Anene, ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a birnin Makurdi.
Wani ganau daya nemi a sakaya sunansa ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, yace hatsarin ya afku ne a wani gida mai daki biyu na unguwar Kwalejin Jesus, gidan mahaifin wadanda abin ya shafa, Mista Ochoche Ode, da misalin karfe 1:00 na safe.
A cewar Ode, ‘yar uwar matarsa ce ta hango gobarar da tsakar daren ranar Juma’a, inda ta ji kamshin cewa wani abu yana ci a lokacin da ‘ya’yansa uku ke barci.
Sannan yace yana daya daga cikin dakunan da matarsa aka sanar dasu lamarin.
“Lokacin da nake shirin gano abin dake faruwa, gobarar ta mamaye duk dakin da yarana ke kwana a kokarin tilasta kaina na shiga dakin domin ceto yaran; fuskata ta yi zafi sosai.
“Duk kokarin da makwabta suka yi na kashe gobarar ya ci tura kuma dukkan ‘ya’yana uku sun kone kurmus,” in ji Ode.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.