Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas LASBCA ta ce, za ta rushe gine-gine guda 70 a cikin jihar.
Guda ashirin daga cikin gine-ginan, suna yankin tsibirin Legas ne wato Island.
Hukumar ta sanar da hakan ne bayan rugujewar wani gida dake hanyar 19 Church, a yankin Island dake jihar.
Mai magana da yawun hukumar ta LASBCA, Mr Gbadeyan Abdulraheem ya ce, Babban Manajan Hukumar Mr Gbolahan Oki ya ziyar ci wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kwara ya Halarci Jana’izar Sarkin Lafiagi
Oki ya ce, ya zama wajibi kuma cikin gaggawa a rushe gine-ginan, wadanda su ka sabawa tsarin rayuwar dan’Adam, domin kauce wa rugujewar su.
Ya kara da cewa, an sanya wa wasu gine-gine alama, domin magance wannan yanayi da ake ciki na rushewar gine-gine.
Kazalika Oki ya ce, Tawagar hukumar ta ziyarci wuraren da lamarin zai shafa, Kuma tuni hukumar ta umarce su, da su canja matsuguni, domin kare rayukar su.
Bugu dakaru Babban Manajan ya ce, Hukumar ta LASBCA ta sanyawa wasu gine-gine guda saba’in a cikin jihar alama, don rushe su.
A karshe Mr Oki ya shawarci al’umar jihar Legas, da su taimaka wa gwamnatin jihar da rahoto kan ginin da akayi, wadanda su ka saba wa ka’ida a yankunan su, domin cima gudurin Gwamnatin na kare rayukar al’uma.