Rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewa, gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita ta tsawon awa ashirin da hudu a ƙananan hukumomin Jema’a da Kaura.
Dama tuni aka kakaba irin wannan dokar a ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf a wani mataki na daƙile rikicin da yake aukuwa a yankin.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren ranar Juma’a bayan da ‘yan bindiga suka kai wani hari a yankunan Jema’a da kuma Maraban Kagoro duk a ƙaramar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
Gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa; dama tun a 2017 aka ƙara kai dimbin jami’an tsaro Kudancin Kaduna bayan da aka gina wani sansanin sojoji a Kafanchan.