Wasan karshe na kasar Kofin Faransa da za a buga tsakanin kungiyar PSG da St Etienne an maida shi zuwa ranar 24 ga watan Yulin 2020, kamar yadda hukumar kwallo kafa ta Faransa, FFF ta tabbatar a ranar Juma’a.
Shi ne zai zama gasar kwararru na farko da za a buga tun bayan dakatar da kwallon kafa a kasar sakamakon annobar cutar Korona.
Shugaban FFF, Noel Le Graet ya ce gasar wanda za a buga tsakanin PSG wadanda suka lashe gasar Ligue 1 bayan an dakatar da kakar wasa ta bana a cikin ranar 30 ga Afrilu. Inda ya kara da cewa mako guda bayan wannan wasan karshen, suma Olympique Lyonnais za su buga na su wasan karshen na gasar League Cup.
Ya ce mutum dubu biyar ne kawai za a bari su shiga filin wasan, kamar yadda Le Graet ya tabbatarwa da FFF.