Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da ranar da komawa makarantu a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Asabar.
Ya ce “dukkan dalibai masu shirin kammala makaranta wanda suka hada da ‘yan firamare Aji 6, JSS 3 da kuma SS3 an ba su izinin komawa makaranta daga ranar Litinin 3 ga watan Agusta, 2020 a duk fadin Jihar.