By Ishaq Dabai
Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta sanar da ranar 17 gawatan Satumba a matsayin ranar da za’a saurari karar masu laifi guda 400 da ake zargi da daukar nauyin masu tada kayar baya.
Idan za’a iya tunawa a watan maris Abubakar Malami ne ya bayyana hakan kan kama wadanda ake zargi na ‘yan kasuwar canji kudade wadan suke canzawa ‘yan kungiyar boko haram kudi
Mafiya yawa daga cikin wasu ‘yan Najeriya suna aiko da kudade daga hadaddiyar daular larabawa zuwa ga ‘yan kasuwar canji kudade BDC.
Alkalin alkalai da Ministan shari’a Abubakar Malami SAN sune suka sanar da hakan inda sukace angama duk wasu tsare tsaren wadanda ake zargi na kaisu kotu da jami’an tsaron farin kaya na jihohi suka kama su.
Idan akayi la’akari da tsaikon da aka samu wajen fara yi musu shari’a, lauyan nan mai zaman kansa Femi Falana SAN ya rubuta takarda zuwa ga Alkalin alkalai na kasa inda ya bukaceshi da a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Falana ya bayyana cewa idan akayi la’akari da wadanda suke daukar dauyin masu tada kayar baya da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami da kashe wadanda basujiba basu gani ba, ba’a gurfanar dasu agaban shari’a ba ya kamata a mutunta su.