Hukumar kwallon kafar Sipaniya ta sanya ranar 18 ga watan Disamba a matsayin ranar da za a buga wasan El-Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona. An sauya masa lokaci daga Asabar din nan mai zuwa sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Catalonia.
Wasan wanda tun da farko aka tsara zai gudana a filin wasa na Camp Nou na Barcelona, La liga ta nemi mayar da shi filin wasa na Real Madrid don gudanar da shi a ranar da aka tsara amma kuma Barcelona ta ki amincewa da matakin.
Yanzu haka dai hukumar La liga ta bayyana cewa za ta shigar da kara kan matakin na hukumar kwallon kafar Sipaniya don kuwa ita ta mika bukatar mayar da wasan ne ko dai ranar 4 ko kuma 7 ga watan Disamba maimakon 18 da hukumar ta zartas.