Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar kulle a jihar, bayan da suka shafe kusan watanni uku a kulle.
Haka ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’i a yayin da yake jawabi ga jama’ar jihar a daren talatar nan.
El-Rufa’i yace bayan sassauta dokar Masallatai da majami’u zasu dinga sallah ne kadai a ranakun juma’a da kuma Lahadi.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-cafke-wani-janar-din-soja-bisa-karya-dokar-kulle-a-kaduna/
Gwamnan ya kuma sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar amma a yanzu babu fita daga karfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na asuba. Wannan sabuwar dokar zata fara aiki ne daga Laraba 10 ga watan Yuni.
Gwamna El-Rufai ya ce bisa ka’idojin da gwamnati ta shimfida, wuraren sana’a za su iya budewa matukar zasu samar da na’urar auna zafin jikin mutum.
Sai dai gwamnan ya ce ba za a bude kasuwanni ba tukunna.
El-Rufa’i ya a kara da cewa, sabon tsarin awannin aiki za su rika farawa daga 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana.