Gwamnatin tarayya tare da ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa da kuma ƙungiyar cigaban ‘yan kasuwa, sun shafe awanni takwas ana tattaunawa dangane da ƙarin kuɗin wuta dana Man fetur ba tare da an cimma matsaya ba.
Ƙungiyar Ƙwadago ta kafe akan lallai sai gwamnatin tarayya ta dawo da farashin man fetur yadda yake a da, ita kuwa gwamnatin ta roƙi ƙungiyoyin su fahimci cewa a yanzu ba ta da ƙarfin biyan tallafin mai kamar yadda take biya a shekarun baya.
Duk da cewa wakilan gwamnatin tarayya sun gabatar da dalilan da yasa aka yi ƙarin wutar lantarkin da kuma farashin man fetur, sai dai duka ƙungiyoyin basu gamsu da dalilan ba.
Sai dai ƙungiyar TUC ta shirya shiga yajin-aikin tare da zanga-zanga a ranar Laraba 23 ga watan Satumbar nan.
Ƙungiyar Ƙwadago kuwa ta bawa gwamantin tarayya tsawon mako guda akan ta dawo da farashin mai yadda yake a baya ko kuma ta tsunduma yajin-aiki.