Jami’an Kwamitin Gwamnatin Kwato Kadarorin Gwamnati karkashin jagorancin Jasper Ndubuaku sun yi kutse cikin daya daga cikin gidajen Uloma Okorocha, diyar tsohon gwamnan jihar Imo domin neman kayayyakin gwamnati da suka zargin an sace an kuma ajiye a gidan.
Sai dai rikici ya barke tsakanin Ndubuaku da Uloma yayin da tawagar gwamnatin ke kokarin kutsa kai cikin gidan diyar tsohon gwmaman.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta kai samame wani kamfani mallakar Uloma Okorocha inda suka rufe wurin bayan kammala bincike.