Ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (HOCSF) ya shawarci ma’aikatan gwamnati da su yi watsi da daftarin, tare da gargadin ma’aikata da su guji kashe albashin su na watan Nuwamba.
Mista AbdulGaniyu Aminu, Daraktan Sadarwa na ofishin HOCSF, ya ba da shawarar a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa shawarar ta zo ne a bayan wata jarida, inda ta yi zargin cewa wata takardar da Dakta Folasade Esan, HOCSF ta bayar, ta shawarci ma’aikatan gwamnati da su yi taka-tsan-tsan wajen kashe albashin su na watan Nuwamba, saboda yiwuwar jinkirin biyan albashi. na watan Disamba.
A cewar Aminu, an ja hankalin ofishin hukumar ta HOCSF kan takardar da aka ce ofishin ya fitar, inda ya shawarci ma’aikatan gwamnati da su yi taka-tsan-tsan wajen kashe albashin su na watan Nuwamba saboda yiwuwar jinkirin biyan albashin watan Disamba.
“Abun takaici an buga labaran karya a wasu jaridu da wasu kafafen sada zumunta ba tare da tantancewa ba. “Don kaucewa shakku, dole ne a bayyana cewa ofishin bai taba bayar da irin wannan daftarin ba game da albashi,” in ji daraktan sadarwa.
Ya cigaba da cewa, wanda ya rattaba hannu kan takardar, wani Dokta S. A. Adegoke ba ma’aikacin ofishin HOCSF ba ne, saboda babu wani jami’in da aka samu a hukumar ta HOCSF.
“Saboda haka, ya kamata a lura cewa, wadanda ke bayan wannan da’awar, kawai suna yin barna ne ta hanyar yada labaran karya saboda dalilan da su suka sani.
“Saboda haka ya kamata a sake jaddada cewa, abun da ake kira da’awar ba komai ba ne illa labaran karya kuma ba a rubuta ko fito da irin wannan da’awar daga ofishin ba,” in ji shi.
Aminu ya shawarci ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a da su yi watsi da abun da ke cikin takardar, karya a matsayin aikin barna. (NAN)