By Abbas Yakubu Yaura
An shiga firgici da tashin hankali a unguwar Emekuku dake Owerri, jihar Imo a safiyar Lahadi bayan da mazauna garin suka wayi gari da ganin gawar wani matashi da wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kashe tare da jefar dashi a bakin hanya.
Wakilinmu ya tattaro cewa mazauna garin sun kwana da fargaba a daren jiya yayin da ‘yan kungiyar asiri ke fafatawa a tsakanin su.
A cewar wani mazaunin yankin mai suna Chinaza Ilechukwu, yace kashe matashin da har yanzu ba a tantance ba ya haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin.
Wani dan jarida mai suna Ilechukwu, ya ce, “Saurayin da ke kwance ba rai an yanka shi a daren jiya a Akalovo Emekuku Owerri a wani abu kamar yakin kungiyar asiri.
Sai dai “An tuntubi sashin ‘yan sanda na Toronto Uratta amma har yanzu basu ce uffan ba kan lamarin, Akwai tsoro a cikin al’umma.
“Wasu shugabannin al’umma sun yi ikrarin cewa an yi kokari da dama don ganin an jawo hankalin ‘yan sanda game da barazanar kungiyar asiri a Akalovo Emekuku amma abin ya ci tura.Sun kuma yi ikirarin cewa an tuntubi ‘yan sanda jim kadan da faruwar lamarin amma har zuwa yanzu babu amsa.”
A martanin da kakakin rundunar ‘yan sandan ya mayar, ya ce za a sanar da jami’in ‘yan sandan shiyya da ke kula da yankin domin daukar mataki.