By Abbas Yakubu Yaura
An samu fargaba a zukatan wasu mazauna garin Osogbo, biyo bayan shigowar shanu kimanin 1,000 karkashin jagorancin wasu makiyaya zuwa cikin babban birnin jihar Osun, da tsakar dare.
Mazauna yankin Omobolanle dake Osogbo, wadanda suka ga dimbin shanun a daren ranar Laraba, sun sanar da jami’an Amotekun cewa garken shanu da makiyaya na zuwa cikin garin.
Da yake amsa wannan kiran na bakin cikin, mutanen Amotekun, karkashin jagorancin kwamandan nasu Amitolu Shittu, an gano cewa, sun tare makiyayan tare da yi musu tambayoyi.
A zantawarsa da wakilinmu a ranar Alhamis, Shittu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce makiyayan basa dauke da makamai, amma ya kara da cewa zuwansu ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.
Sannan ya ce, “Gaskiya ne wasu makiyaya da suka taho daga Ogbomoso sun shiga Osogbo da tsakar dare. Makiyaya 12 ne suke jagorantar shanu kusan 1,000.
Sannan yace “Da farko basu so ba da hadin kai ba, amma bayan mun hana su tafiya, sai suka ce suna neman ruwan shayar da dabbobin sune. Sun kuma shaida mana cewa da rana sun yi ta zagaye garin domin gano hanyoyin da suke son bi.
“Mun sanar da su cewa jihar Osun ta haramta kiwo a fili, Sai muka kai su ga wani kogi.Bayan shanunsu sun sha ruwa, sai muka yi tattaki dasu zuwa kan iyaka tsakanin Osun da wata jiha mai makwabtaka. Kasancewarsu ya haifar da firgici amma mun yi gaggawar kama lamarin.”