By Abbas Yakubu Yaura
A jiya ne aka samu barkewar rikici a yankin Omuanwa dake karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas yayin da wani daga cikin gungun ‘yan sintiri a yankin ya kashe wani jami’in sojin saman Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin mazauna unguwar, sun gudu daga yankin saboda fargabar ramuwar gayya daga rundunar sojojin saman Najeriya.
Wata majiya a yankin da ta bayyana mamacin mai suna Chinedu Endurance, ta sanar da cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, inda ta ce wadanda suka aikata kisan ‘yan kungiya ne na kwamitin samar da zaman lafiya da ba da shawara kan harkokin tsaro na Omuanwa, OSPAC.
Wani dan yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da ‘yan kungiyar sintiri na yankin suka yi kaca-kaca da wasu mutane musamman matasa tare da tursasa su wajen yin rantsuwa.
Majiyar ta ce matsalar ta tabarbare ne a lokacin da aka kama wani dan uwa ga jami’an Sojin sama, Endurance, aka yi masa dukan tsiya, aka ajiye shi a dakin ajiyar OSPAC.
Sannan ya ce jami’an sojin sama sun tunkari OSPAC domin jin laifin dan’uwansa, amma an harbe shi aka kai shi asibiti inda daga baya ya mutu.
A halin da ake ciki kuma, ‘yan sanda a jihar sun tabbatar da kama wani dan kungiyar sintiri da ya kashe jami’an sojin sama
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a jiya ne shugabannin al’ummar yankin suka mika wanda ake zargin, Progress Emecheta, ga rundunar ‘yan sanda da ke Isiokpo kafin a mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, SCID.
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, PPRO, Grace Woyengikuro, a wata ‘yar gajeriyar sanarwa ta ce, “Akan lamarin da ya faru a Omuanwa, an kama jami’an OSPAC mai suna Progress Emecheta.Ana tsare da wanda ake zargin a hukumar ta SCID kuma ana ci gaba da bincike.”