Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tafiya jinya zuwa Burtaniya Kuma har yanzu yana kan hanya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mutane da dama sun bayyana mamakinsa bayan da shugaban ya koma kasar a ranar Juma’a, maimakon ya nufi birnin Landan kamar yadda aka sanar tun da fari.
Shugaban wanda ya halarci bikin cika shekaru 50 da kafa Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) a birnin Nairobi na kasar Kenya, ana sa ran zai wuce Birtaniya domin duba lafiyarsa na tsawon makonni biyu.
Femi Adesina, mai magana da yawun Buhari ne ya sanar da ziyarar a cikin wata sanarwa da ya fitar a farkon makon nan.
“Daga Kenya, Shugaba Buhari zai wuce Landan domin duba lafiyarsa na tsawon makonni biyu,” in ji Adesina.
Sai dai an dan samu rudani a ranar Juma’a lokacin da Bashir Ahmad, mai taimaka wa Buhari, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shugaban ya dawo Nigeria.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja, bayan halartar bikin cika shekaru 50 da kafa hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) a birnin Nairobi na kasar Kenya,” ya rubuta a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad a ranar 4 ga Maris, 2022.
Wasu masu amfani da shafin Twitter sun nuna kaduwa, suna neman a yi musu bayani kan ci gaban da aka samu saboda ba a bayar da wata sanarwa a hukumance ba.