Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare a Najeriya ta ce ta fasa yin amfani da lambar katin shaidar dan kasa ta NIN yayin gudanar da jarrabawarta a shekarar UTME ta 2020.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta Farfesa Ishak Oloyede a ranar Asabar a wani taron manema labarai a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
Farfesan ya ce matakin soke amfani da lambar a matsayin rukuni na rubuta jarrabawar UTME ya zo ne bayan kiraye-kiraye daga masu ruwa da tsaki.
Farfesa Oloyede ya bayyana cewa: “Mun amince mu jingine amfani da ita saboda wasu matsalolin da suka sha kanmu na daban”.
Ya kara da cewa: “Mun yanke shawarar jingine amfani da lambar NIN ne a jiya (Juma’a) a matsayin wani rukuni na rubuta jarrabawar UTME ta 2020 da kuma rajistar Direct Entry (DE) har sai 2021.
“Zuwa lokacin za a bai wa kowane dalibi wa’adin shekara guda domin ya yi rajistar (lambar NIN).
“Mun bincika mun ga yadda dalibai suka zaku su rubuta jarrabawar. Mun fahimci cewa abin da muka tsammata ba zai samu ba a yanzu, saboda ba za mu matsa wa dalibai ba.”
Farfesa Oloyede ya kuma bayyana cewa daya daga cikin dalilansu na soke tsarin shi ne na yadda hukumar NIMC, mai bayar da katin shaidar dan kasa, take gudanar da yin rajistar ga mutane.
Saboda haka ya ce suna kokarin kaddamar da wani shiri domin bayar da rajistar cikin sauki.
Dalibai a Najeriya suna rubuta jarrabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ne yayin da suka kammala makarantar sakandare, wadda da jarrabawar ce za su shiga kwalejoji ko kuma jami’o’i.
Dalibai sama da miliyan daya ne ke rubuta jarrabawar a duk shekara a fadin kasar.