Hukumar gudanar da jami’ar Bayero Kano (BUK) ta tabbatar da Farfesa Sagiru Abbas a matsayin sabon shugaban da zai jagoranci jami’ar.
Takardar tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban, wanda Pro-Chancellor da kuma shugaban hukumar gudanar da jami’ar, Farfesa Gambari suka sanyawa hannu, an mika wa sabon shugaban jami’ar ne a ranar Asabar a Kano.
A cikin takardar, Farfesa Gambari ya shaida cewa Farfesa Abbas zai yi wa’adin mulki daya ne mai tsawon shekara biyar, wanda zai fara daga 18 ga watan Agusta.
Abbas, wanda yake Farfesa ne a tsangaya ilimi (education), an zabe shi ne a wannan mukamin a zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa ya samu kuri’a 1,026, inda kuma Adamu Tanko ke biye da shi da kuri’a 416. Sauran ‘yan takarar sun hada da; Mohammed Dikko da Dalhatu Balarabe da suke da kuri’a 10 da kuma 5.
Da yake maida jawabi, sabon shugaban jami’ar, ya roki al’ummar Jami’ar da su ba shi dukkannin goyon baya wajen ganin ya ci gabantar da jami’ar gaba. Inda ya bayar da tabbacin cewa; zai yi dukkanin abin da zai iya wajen ganin ya kawo wa jami’ar ci gaba ta hanyar tafiya da kowa da kowa.