Jami’an ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu ‘yan fashi har su uku bayan da aka tafka gumurzu.
Masu laifin sun hada da Toheed Salami, Ibrahim Ismaila da Michael Abiodun, kuma an yi nasarar kama su ne bayan da aka sha gumurzu dasu a ranar lahadi.
Kakakin hukumar’yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
Oyeyemi yace sun samu kiran agaji ne inda aka bayyana musu cewa ‘yan sun shiga yankin Idanyin dake karamar hukumar Agbara, Ado-Odo/Ota ta jihar Ogun.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-shugaban-jamiyyar-apc-a-katsina/
Yace sun samu rahoton ‘yan fashin na shiga gidajen mutane suna kwace kayansu tare da raunata wasu.
“Suna hango jami’an ‘yan sanda sai suka far musu da harbi, amma an yi nasarar kama uku daga cikin, dayan kuma ya tsere”.
“Daga cikin abinda muka kama su dasu sun hada da bindiga kirar hannu, sai dai mun dauke su zuwa asibiti sakamakon raunukan da suka samu a yayin gumurzun da aka yi da su”.
Oyeyemi ya kara da cewa, shugaban hukumar’yan sanda na jihar Kenneth Ebrimson ya umarci a mika su zuwa sashen kula da manyan laifuka domin yin cikakken bincike akansu.