An Tallafi waɗanda Ambaliyar Ruwa ta Shafa da Kayan Abinci na Miliyan 19 a Jigawa
Kimanin mutane 1,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa sun samu tallafin kayan abinci na Miliyoyin naira daga hannun wani dan majalisa.
Mamba mai wakiltar mazabar Buji/Birnin Kudu a jihar Jigawa, Injiniya Magaji Da’u a kwanakin baya ya bayar da tallafin kayayyakin da kudinsu ya kai Naira miliyan 19 ga wadanda ambaliyar ruwa ta lalata da ‘yan uwansu da gidaje da gonakinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Na Da Abubuwan Sambarka Yayin Cika Shekaru 62—- Gwamnan Gombe
Da yake jawabi a lokacin bikin kaddamar da rabon kayayyakin a Jigawa, Hon Magaji ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya kuma bukace su da su dauki wannan Iftila’in a matsayin kaddara, ya kuma kara da cewa munanan illolin da ambaliyar ta haifar a bayyane take, kuma wadanda abin ya shafa na matukar bukatar taimako.
“Hakki ne a kaina da duk wani mai hannu da shuni na ba da gudummawa ga ƙoƙarin gwamnati na samar da kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa. Suna cikin wannan hali ba wai don sun ba da izini ba sai don Allah ne ya kaddara faruwar hakan,” inji shi.
An mika tallafin kayan abinci ga hakimai tara na yankunan da abin ya shafa domin rabawa wadanda abin ya shafa a yankinsu.
A wani labarin kuma: Cikin wani yanayi, Buhari ya ce yana jin raɗaɗin halin da ƴan Najeriya ke ciki
A yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana jin radadin halin da ƴan Najeriya ke ji, akan ƙalubalen da ake fuskanta da ke ci gaba da fuskantar al’umma.
Sai dai kuma ya ce gwamnatinsa ta cika mafi yawan alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya a zaben 2015 da 2019.