Kasurgumin dan rajin raba Najeriyar nan Sunday Igboho zai shafe wa’adin karshen makon nan a gidan yarin kasar jamhuriyyar Benin bayan da kotun daukaka kara ta kasar ta dage sauraron shari’arsa sai mako mai mai zuwa.
Ko da yake tun ranar Alhamis ne kotun ta ɗage shari’ar sai zuwa ranar juma’a, to amma sakamakon rashin zama da kotun ta yi ya sa aka ci gaba da tsare shi har sai makon gobe.
Da ma dai ana zargin Igboho ne da laifi shiga kasar ta haramtacciyar hanya.
Rahotanni sun bayyana cewa har kawo yanzu babu takamaiman ranar gudanar da shari’ar tasa, amma Ƙungiyar ta Ilana Omo Oodua ta ce ranar Litinin ce za a gurfanar da shi gaban kuliya.
Da ma dai kungiyar karkashin tsohon Sanata Banji Akintoye ta kasance yayin shari’ar don ganin yadda take gudana.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne Kotun ta kasar jamhuriyyar Benin ta yi hukunci kan sakin matar Igboho wacce yar asalin ƙasar Jamus ce, amma kuma ta bada umarnin garkame mijin nata har sai ranar da aka dawo sauraron karar.