An tono wani dadden masallaci da ake kyautata zaton yakai shekaru 1200 a birnin Raht dake kasar Israela.
An gano masallacin ne a lokacin da ake kokarin gina wata unguwa a birnin Raht dake kasar Israela.
Kungiyar kula da kayan tarihi ta kasar ta bayyana cewa masallacin yana da shekaru 1200 wato shekarun farkon addinin musulunci kenan.
Haka dai birnin ya kasance karkashin kulawar Palastinawa inda akayi ginin masallaci a karni na 7 da kuma karni na 8.
Kazalika bincike ya tabbatar da cewa manoma ne ke amfani da masallacin a lokacin.