By Abbas Yakubu Yaura
Wata Kotun Majistare ta Jihar Ekiti da ke gundumar Ado Ekiti ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai suna Ayodeji Abiola mai shekaru 35 bisa zargin kashe mahaifiyarsa mai shekaru 75 mai suna Florence Abiola.
Wanda ake tuhuma yana fuskantar tuhumar kisan kai.
Dan sanda mai shigar da kara, Olasunkanmi Bankole, a cikin wata bukata ta farko, ya roki kotun data tasa keyar wanda ake kara zuwa gidan yari.
Hakan, a cewarsa, zai baiwa ‘yan sanda damar kammala cikakken bincikensu, yayin da za a mika kwafin fayil din karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a na jihar.
Takardar ta kara da cewa, “Abiola Ayodeji ana zarginsa da aikata laifin kisan kai ga mahaifiyarsa mai shekaru 75, Abiola Olaitan Florence, a ranar 11 ga watan Janairu, 2022, a Ipole Iloro a gundumar Aramoko Ekiti. Laifin ya sabawa hukuncin a karkashin sashe na 319 (1) na kundin laifuffuka, C16,na Dokokin Jihar Ekiti shekarar 2012.”
Wanda ake tuhumar ya fito daga Ipole Iloro da ke karamar hukumar Ekiti ta Yamma a jihar Ekiti, a cikin sanarwar da ya yi wa ‘yan sanda ya ce sun samu rashin fahimtar juna da mahaifiyarsa a ranar da lamarin ya faru, kuma a lokacin da ya bugeta da sanda a kai, wanda ya yi sanadin mutuwarta, yayin da ya jefar da gawar ta a cikin daji.
Alkalin kotun mai shari’a Titilayo Olaolorun, wanda ya amince da bukatar mai gabatar da kara, ya ce, “An bayar da umarnin tsare wanda ake kara a gidan yari na Najeriya, Ado Ekiti, na tsawon kwanaki 30, har sai an kammala binciken ‘yan sanda.”
Olaolorun ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun 2022 domin ambatonsa.