Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa jihar Ebonyi domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar.
Shugaban wanda ya samu rakiyar gwamna David Umahi na Ebonyi da wasu manyan jami’an gwamnati sun isa jihar da misalin karfe 11:15 na safe.
To sai dai titunan babban birnin jihar Makare yake da jami’an tsoro domin tabbatar da kwanciyar hankali, baya ga zaman lafiya.
Jirgin mai saukar ungulu dauke da shugaban kasa mai lamba: 5N-FG1 ya sauka a rumfar da ke cikin gidan gwamnan a mahaifarsa, Uburu, karamar hukumar Ohaozara ta jihar.
Shugaban bayan ya yi musabaha da manyan jami’an gwamnati, da sarakunan gargajiya da sauran wadanda suka zo tarbarsa, ya duba wani harsashi da rundunar sojin Najeriya ta dora.
Shugaban kasar zai bude babbar jami’ar King David ta kimiyyar likitanci da ke Uburu tare da tituna da gadar sama da sabon dakin zama na shugaban kasa a Abakaliki.
Ana kuma sa ran shugaban kasar zai kaddamar da babbar cibiyar kasuwanci ta kasa da kasa ta Ebonyi, da kayayyakin aiki a sabon gidan gwamnati da aka gina, da kuma ayyukan tituna a jihar da dai sauransu.