An tsaurara matakan tsaro a muhimman guraren birnin Kano inda ‘yan sanda suka toshe hanyoyin shiga gidan gwamnatin jihar Kano da kuma barikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma dake Hotoro, kan titin zuwa Maiduguri.
Wata jarida ta yanar gizo ta Daily Nigerian a ranar Juma’a ta ruwaito cewa an ji karar harbe-harbe a hedikwatar ‘yan sanda ta Zone 1 da ke kan titin BUK cikin kwaryar birnin Kano.
Jaridar ta ce ‘yan ta’addan sun zo ne a cikin motoci uku da misalin karfe 12:30 na ranar Juma’a inda suka yi harbi da yawa a ginin sannan suka kara zube.
KARANTA KARIN WANNAN LABARIN: Babachir Lawan ya roki yan Najeriya kan kada su zabi Tinubu
Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata labarin da ke cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai hari a shalkwatar rundunar ‘yan sandan da ke Kano.
Da yake mayar da martani, jami’in hulda da jama’a na ofishin shiyya ta daya a Kano, Abubakar Zayyanu Ambursa, ya musanta harin.
A lokacin da yake zantawa da manema Labarai, Ambursa ya musanta batun duk wani harin ta’addanci da aka kai ofishin.
“Babu wani abu kamar harin da aka kai, domin ina ofishina da na ga labari, sai na je bakin kofar shigowa na tabbatar da abin da aka fada, amma ban ga makamancin haka ba ( wato harbe harben).
Jami’in hulda da jama’a ya kara da cewa akwai wasu jami’ai na musamman da aka saba jibge a kofar hedikwatar shiyya a ranar Juma’a kuma tabbas daga gare su ne ya fito; “Akwai jami’ai na musamman da muke ajiyewa a kan hanya duk ranar Juma’a, amma ko da na je can, sun gama aikinsu sun bar wurin.
Sai dai masu gadin kofar shiga da na samu, kuma sun tabbatar min da cewa babu wani abin ban tsoro da ya faru a wurin”.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan ainihin abunda ya faru a shiyyar yan sandan ta daya.