An tsaurara matakan tsaro a gidan Sanata Ibrahim Shekarau sakamakon kona ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin, mai neman tsayawa takarar gwamna a zaben 2023.
Jibrin, daya daga cikin jigo a jam’iyyar APC ta Kano G-7 karkashin jagorancin Shekarau, Jibrin, yana wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa.
Kungiyar G-7 ta samu gagarumar nasara a ranar Talata lokacin da wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta amince da zababbun shugabannin da aka zaba a gundumominsu amma ta rusa wadanda bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya zaba.
An ce wasu batagarin Matasa a masu yawa sun kai hari a ofishin yakin neman zaben da ke kan titin Maiduguri a yammacin ranar Laraba.
Ginin da abin ya shafa mallakin tsohon Ministan Kwadago, Alhaji Musa Gwadabe ne.
Gidan Sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar da kuma gidan Shekarau na karkashin kulawar yan sanda saboda fargabar wasu ‘yan bindiga ka iya kai musu hari.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa domin jin ta bakinsa game da lamarin, ya ce a halin yanzu suna tattaunawa kan lamarin.
Amma kwamishinan ‘yan sandan Ismaila Dikko, ya ce tuni mutanen sa suka karbe Iko wurin.
Lamarin ya faru ne sa’o’i bayan da aka kulle daya daga cikin ofishin lauyoyin da ke wakiltar bangaren Shekarau a Kano.
Comments 1