By Abbas Yakubu Yaura
An jibge jami’an tsaro sosai a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano a shirye-shiryen isar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar.
Ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da taron makon sojojin saman Najeriya a Kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta lura cewa an yiwa titin da ke zuwa fadar Sarkin Kano kawanya tare da jibge jami’an tsaro da muggan makamai a kan titin da motocinsu.
A fadar sarkin, daruruwan jami’an tsaro dauke da muggan makamai da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaro na farin kaya, sojojin Najeriya, da sauran su ne suke jibge a kofar gidan da kewaye da motocinsu, ciki har da motocin EOD daga fadar gwamnati. .
Sai dai an hana ‘yan jarida shiga fadar, inda ake sa ran shugaban zai ziyarta kafin ya nufi wurin taron makon rundunar sojojin sama.
Jaridar Dimokuradiyya ta ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata an samu fashewar wani abu a unguwar Sabongari da ke jihar Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu da dama.
Kwanaki biyu bayan fashewar bom din, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata mota makare da kayan fashewa, bindigu da alburusai.
Kazalika rahotanni sun bayyana cewa an samu rashin jituwa tsakanin mazauna yankin da ‘yan sanda kan abin da ya kai ga fashewar inda mazauna yankin suka ce harin bam ne yayin da ‘yan sandan suka ce duk wata shaida na nuna fashewar iskar gas da sinadari.