Shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya tsige Firaministan kasar kana da ya dakatar da majalisar kasar baki ɗaya biyo bayan wata zanga-zanga da aka yi ranar Lahadi.
Zanga-zangar wacce ta biyo bayan fusata da jama’a suka yi game da yadda gwamnati ke rikon sakainar kashi wa harkar cutar korona ta yi sanadiyar cafke daruruwan mutane tare da tsayar harkoki cak.
Shugaba Kais Saied wanda aka zabe shi a shekara ta 2019 ya ce zai maye gurbin firaministan lamarin da ya kai ga magoya bayansa murna baki har kunne, sai dai yan adawa a majalisar sun zarge shi da yunkurin juyin mulki.
Juyin juye halin shekara ta 2011 da ya bazama zuwa wasu ƙasashen Larabawa ya yi sanadiyar salwantar dukiyoyi.
Kazalika a makon da ya gabata shugaba Kais Saied ya tsige Ministan Lafiyar kasar sakamakon yadda aka gudanar da rigafin korona ba bisa ka’ida ba lamarin da ya haifar da halin ɗar-ɗar a kasar.