An tsige Shugaban karamar hukumar Langtang ta Arewa reshen jihar Filato Honorabul Bitrus Zulfa Rimven.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Mambobi 14 daga cikin 18 na majalisar dokokin karamar hukumar ne suka amince da tsige Mr Rimven.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Wasu A Ma’aikatar Kudi Ta Bauchi Suka Rabe Kudin Wani Mamaci N332,000 A Tsakaninsu
Wata majiya daga karamar hukumar ta shaida wa Majiyar Dimokuradiyya cewa, an gudanar da ayyukan tsigewar ne ta hanyar kada kuri’ar yankan kauna a zaman majalisar na ranar Talata.
Majiyar ta ci gaba da cewa, tsige shi ya biyo bayan sanarwar da aka yi na zargin aikata manyan laifuka da ake wa tsohon shugaban, wanda majalisar ta sanar da shi zarge-zargen makonni biyun da suka gabata.
A WANI LABARI KUMA: Dan bindiga Ya Harbe Wani Shahararren Mawakin Amurika Har Lahira
An harbe wani mawaki dan kasar Amurka, Rakim Hasheem Allen, AKA PnB Rock har lahira.
Daily Post ta ruwaito cewa, An harbe PnB Rock a wani fashi da makami da aka yi a Kudancin Los Angeles na Amurka a daren jiya Litinin.