Basaraken gargajiya na yankin Ihitte Ihube mai cin gashin kansa a karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, Paul Ogbu, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da Yan bindiga suka babbaka fadarsa da motarsa, an gano gawarsa.
An kuma tsinci gawar wani shugaban matasa a yankin wanda shi ma aka yi garkuwa da shi tare da sarkin da aka kashe.
A yau (Alhamis) ne za a yi jana’izar basaraken gargajiyar kamar yadda aka kai gawarsa masarautarsa ranar Laraba.
Majiyoyin al’umma da suka bayyana wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya a ranar Alhamis sun bayyana cewa wani basaraken gargajiya Acho Ndukwe ne da aka yi garkuwa da shi tare da Ogbu wanda ya bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwa da su sun kashe Ogbu.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce, “An tsinci gawar Eze Paul Ogbu da shugaban matasan yankin Eze Acho Ndukwe, ya bayyana cewa masu laifin sun kashe Eze Paul Ogbu a gabansa. Jami’an tsaro sun koma sansanin ‘yan ta’addan tare da ‘yan mutanen yankin, inda aka gano gawar basaraken gargajiyar tana kwance a cikin wani rami. Za a yi jana’izarsa yau Alhamis.”
Idan za’a iya tunawa dai, An yi garkuwa da Ogbu da Ndukwe ranar Lahadi tare da kona motocinsu da kuma fadar basaraken.
An kubutar da Ndukwe ne a ranar Litinin bayan da jami’an tsaro suka hada kai suka kai samame a rukunin masu aikata laifuka a karamar hukumar Orsu da Uli a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan ya ce shi bai sani ba kuma zai yi min bayani idan ya gane
Comments 1