An tsinci gawar wani Darakta a ma’aikatar gwamnatin jihar Ondo da ya bata tun ranar Alhamis din da ta gabata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an gano gawar babban ma’aikacin gwamnati mai suna Mista Gbenga Olofingboyegun a yau Lahadi amma a mace kuma an yanke kai.
Olofingboyegun, wanda shi ne Daraktan Sashen Bincike da Kididdiga, a Hukumar Kula da Ayyukan Koyarwa (TESCOM), an bayyana bacewarsa a ranar Alhamis bayan ya bar ofishin saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Bayan bacewarsa kwatsam ‘yan uwa da abokan arziki sun yi zargin cewa masu garkuwa da mutane ne, suka yi garkuwa da shi.
Kafin a gano gawarsa, dangin sun dade suna jiran kiran wadanda ake zargin sun sace shi domin a biya shi kudin fansa.
KARANTA ANAN: Nasarar Atiku Abubakar A 2023, Zata Farfaɗo Da Tattalin Arzikin Najeriya – Tambuwal
An tsinci gawar sa ne a makarantar firamare ta Saint Theresa daura da makarantar Saint Peter’s Unity School dake Akure.
A cewar majiyoyi, an yanke kan Olofingboyegun tare da yayyaga cikinsa wanda kuma ake zargin maharan ne suka aikata masa hakan.
Wata majiya daga iyalan marigayin ta ce har yanzu marigayin na cikin kayan aiki na ofishinsa da ya saka a lokacin da aka gano gawarsa da ta rube.
A halin da ake ciki, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Funmilayo Odunlami, ya ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan gawarsa.
A wani labarin kuma: Ku Sanya Bukatun Al’ummar Kano A Gaba Sama Da Bukatar Kai – Farfesa Munzali
Fitaccen masani kuma malamin turancin nan farfesa Munzali Jibril ya ce koyar da dalibai cikin harshen Hausa shi ne kadai mafita ga matsalar ilimi a Arewacin kasar nan.
Munzali Jibril ya bayyana hakan ne yayin taron wuni daya da dukkanin yan takarar gwamman a dukkanin jam’iyyu domin gabatar musu da manufofin da za su ciyar da Kano da Jigawa gaba.