By Abbas Yakubu Yaura
An tsinci gawar wani fasto mai suna Segun Adebisi a wani gini da ba a kammala ba a Kubwa,dake a Abuja.
Mazauna yankin sun gano hakan ne a safiyar ranar Asabar a yayin da suke bincike bayan an bayyana bacewarsa.
Jigawa: INEC Ta Ce Katin Masu Zabe Na PVC Dubu 33 Sun Kammala
Wani mazaunin garin Odion Rufus ya shaidawa City & Crime cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda yayin da ‘yan uwa ke ta kai komo na neman faston.
Rufus ya ce, “A cikin satin, mun watsu zuwa cikin daji da ke kusa da wurin dan fadada neman sa daga karfe 8 na dare har zuwa karfe 12 na safe amma ba mu iya gano shi ba.
“A safiyar ranar Asabar, mun sake gudanar da wani bincike a kusa da wurin farko, kuma muna cikin shirin yin kasa a gwiwa ne, sai daya daga cikin mu ya ba da shawarar cewa mu mika binciken zuwa wani gini da ba a kammala ba.
“Mun hadu da gawarsa da raunuka a kansa kamar an buge shi da wasu itacen da aka samu a kusa da gawar.
“An kai gawarsa dakin ajiyar gawa na asibin yanki.”
Kawo yanzu dai babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Wannan dai bashi ne karon farko da ake samun gawarwaki a yashe a sassa daban daban na kasar ba a wasu muhimman wurare kama daga Otel da makamatan su.
Comments 1