An tsinci kan wani jami’in ‘yan sandan kasar Kamaru ba tare da gangar jikinsa ba a birnin Bamenda, hedikwatar yankin Arewa maso Yamma, daya daga cikin jihohin kasar da ake amfani da Turancin Ingilishi mai fama da rikicin ‘yan aware.
Majiyar tsaron Kamaru dai ta daura alhakin kissan jami’an dan sandan Paul Nwana, a daren Lahadi, kan mayakan ‘yan aware dake neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia.
Rahotanni sun ce kan jami’in tsaron yana dauke raunuka da dama, abin da ke nuna alamun cewar an azabtar da dan sandan kafin a yi masa kisan gillar.
Wannan na zuwa ne kasa da makwanni uku, bayan kisan gillar da aka yi wa Frorence Ayafor jami’ar tsaron gidan kaso, ita ma a birnin na Bamenda, matakin da ya kai kashen duniya suka yi Allah wadai da shi.