A ranar Talatar data gabata ne jami’an tsaro suka kama daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin Arewa, Sheriff Nastura Ashir, bayan ya da jagoranci wata zanga-zangar lumana da aka yi a jihar Katsina.
An gudanar da wannan zanga-zangar ne domin nuna alhini akan rashin tsaro da ya yi kamari a kasar da kuma yawan kashe-kashen da ake yi wa farar hula, musamman a shiyoyin Arewa ta yamma da Arewa ta gabas da suka kunshi jihohin Kaduna, Neja, Katsina, Zamfara, Sokoto, Taraba, Adamawa, Yobe da kuma Borno.
Nastura ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da Muryar Amurka tayi da shi a daren ranar Alhamis, Nastura ya ce an tuhume shi da laifin shirya zanga-zanga ba tare da izinin hukumomin tsaro ba, kuma an zarge shi da zagin daya daga cikin masu magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adeshina.
Nastura ya ce sun nuna wa jami’an tsaro takardar neman izinin da suka aika wa Sufeto Janar na ‘yan sanda Najeriya da kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina mai dauke da tambarin da ya nuna an sa hannu an kuma karbi takardar tun kafin ranar da aka yi zanga-zangar.
“Jami’an ‘yan sanda sun kula da ni a cikin kwanaki biyu da wuni daya da na yi a hannunsu kuma ba su wulakanta ni ba, a cewar Sherif.
Har wa yau, Nastura yace yaƙi amincewa da yaci abincin da jami’an tsaro suka kawo masa saboda tsaro da kuma irin shwarwari da ya ɗauka daga makusanta shi.