Gwamnatin jihar Kano ta ware miliyan 800 domin magance matsalar talauci da rashin aikin yi a tsakanin mata da matasa a fadin jihar.
Kwamishinar harkokin mata da cigaban al’umma ta jihar Dr. Zahra’u Muhammad Umar ta bayyana hakan a zauren majalisar dokokin jihar Kano yayin da take kare kasafin kudin ma’aikatar ta shekarar 2022.
Dr Zahara’u ta ce ana gyare-gyare a cibiyar gyaran hali da tarbiya ta Kiru tare da fadada girmanta yadda za a rika horar da masu shaye-shaye maza da mata su zama masu amfani a cikin al’umma.
Haka kuma ma’aikatar ta za ta mayar da hankali wajen horar da mata da matasa a 2022 karkashin shirin gwamnati na bayar da tallafi daga matakin farko. Kimanin Naira miliyan 800 aka ware domin fara aikin daga matakin farko da nufin magance talauci da rashin aikin yi, kuma wadannan abubuwa biyu (talauci da rashin aiki) sune manyan matsalolin da ke addabar cigaban mutane.
Kwamishiniyar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya dabaru da nufin farfado da kayan sana’ar cikin gida, kamar man gyada da ake sarrafawa a gida da kuma kayan cincin da mata ke yi a yankunan karkara domin dogaro da kai.