Wasu fusatattun masu zanga-zanga a kasar Canada sun kakkarya mutum-mutumin sarauniya Victoria da aka kafa a kasar.
Wannan aika-aika ya biyo bayan mace macen yara da ake samu ne a makarantun kasar da aka alakanta da Birtaniya.
Kazalika masu zanga-zangar sun wargaza mutum-mutumin sarauniyar Ingila Wato sarauniya Elizabeth.
Kafafen watsa labaran kasar sun ruwaito cewa masu yan sanda sun kama mutumin dake da hannu wajen kitsa zanga-zangar, wanda aka ce ta lumana ce.
Wannan mummunar aiki da aka yi ya zo ne daidai da bikin ranar Canada da ake yi, don tunawa da kirkiro kasar da turawan mulkin Birtaniya suka yi a shekarar 1867.
Comments 1