Daga Haji Shehu
Da yake bankwana da alhazan jihar Kano jirgi na karshe, Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nunawa Alhazan tsananin bukatar sanya Najeriya cikin adduar zaman lafiya Mai daurewa.
Yayinda yake jawabi ga Alhazai 330 ciki harda mukarraban gwamnati da kuma masu lura da lafiyar mahajjatan jihar a filin tashi da saukan jiragen sama na tinawa da Malam Aminu Kano dake jihar Kano, gwamna Ganduje ya nuna tsananin bukatar rokawa Najeriya da jihar Kano zaman lafiya. Gwamnan ya kara da cewar “Kar ku mance da yin adduar zaman lafiya, Hadin kai, da Cigaban kasar mu. Bayan haka, kar ku manta da gwamnan ku da kuma gwamnatin jihar Kano a cikin adduar ku.
Gwamna Ganduje ya roki mahajjatan da su kasance wakilai na kwarai wa jihar Kano a dukkanin harkoki da ibadun da zasu gabatar a kasa mai tsarki, Gwamnan ya roki Alhazan da su kaucewa aikata duk wani abunda zai dakushe mutuncin jihar. Bugu da kari gwamnan ya gargadi mahajjatan da su zama masu bin doka da oda da kuma bin dukkanin sharruda da hukumar aikin hajji ta gindaya.
A cikin jawabin sa gwamna Ganduje ya shaida cewar gwamnati ta shirya tsaf domin ladaftar da duk wani mahajjacin da yayi ko yake kokarin aikata abunda zai dakushe mutuncin jihar Kano a kasa mai tsarki. Gwamna Ganduje ya cigaba da cewar “Muna kira gareku da ku sadaukar da lokutan ku da damar ku wajen yin adduoi da kuma zama wakilan kirki ga jihar Kano. Duk wanda aka samu da aikata wani mummunar dabia, hukumomi a kasar saudiya sun shirya Kotu ta musamman wanda zata ladaftar dasu, sannan kuma su dawo gida Najeriya mu kara ladaftar dasu.
Babban Sakataren hukumar jindadin Alhazai na jihar Kano, Alhaji Mohammad Abba Danbatta ya shaidawa gwamnan cewar tare da tashin wannan rukuni na karshe daga jihar Kano zuwa kasa mai tsarki, hukumar tayi nasarar kwashe Alhazai 3,170 daga jihar Kano zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin hajjin shekarar 2019.
Alhaji Abba ya bayyana godiya tare da jindadin su ga gwamna Ganduje bisa yadda gwamnati ta inganta masauki, abinci, sufuri, lafiya da kuma walwalar mahajjatan jihar Kano a kasa mai tsarki.