An yakewa Habiba Abubakar shekaru bakwai gidan Kaso
Hukumar EFCC reshen Jahar Kano sun kama Habiba Abubakar, inda suka migata gaban mai Shari’a J.K Daggard dake babban Kotu ta Kano kan tuhumarta da akeyi da damfara.
Ana tuhumarta ne da sayar da wani babban fili, inda ta baiwa mai sayen takardar bogi.
KARANTA:- Yan sanda Sun kubutar da Mai bai wa Gwamnan Cross Rivers Shawara
Wanda ya kawo korafin yace “ta nemishi da sayen wani fili dake Rijiyar Zaki a Kano.”
Inda take ikirarin ta saka filin a kasuwa ne saboda ta sami abinda zata dauki dawainiyar marayun yaranta guda bakwai.
Mai korafin yace, ta sallama masa filin kan kudi miliyan biyu da dubu dari biyu, sai ya bata Motoci kimanin wadannan kudaden shi kuma ya mallaki filin.
Ananan sai wani da ake Kira Balarabe, yazo yana cewar ai filinnan nasa ne.
Sai daga baya aka gane cewar takardun da ta bayar ashe na boge ne.
Lokacin da aka tuntube ta tace ita bata da laifi, nan take Shari’a ta soma.
Sai lauyan Mai korafi Musa Isa ya gabatar da kwararren shaidu guda hudu, tare da gabatar da takardun gamsassu.
A dai ranar Talata ne, Mai Shari’a J.J Daggard ya tabbatar da wanda yake korafi shine mai gaskiya.
Nan take Mai Shari’a ya yanke Mata hukuncin shekara bakwai gidan Kaso.
Tare da umartar ta data biyashi naira miliyan biyu da dubu dari tara.