By Abbas Yakubu yaura
Akalla mutane 124 aka kama tare da yanke musu hukuncin wadanda suke yiwa al’umma aiki bisa samunsu da laifin yin bahaya a fili a jihar Ogun.
Mai ba Gwamna Dapo Abiodun shawara na musamman kan muhalli kuma babban jami’in hukumar kula da sharar gida ta jihar Ogun (OGWAMA), Ola Oresanya ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Alhamis a Abeokuta.
A cewarsa, an kama wadanda suka aikata laifin a sassa daban-daban na jihar tare da kama 82 daga cikin su a yankin Mowe-Ibafo dake karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar.
Oresanya ya gargadi direbobin ababan hawa da ’yan kungiyarsu dasu daina yin bahaya a tsakar gida da bakin titi yayin da suke kan hanya.
Sannan ya bukace su da su rika ziyartar gidajen jama’a da gwamnatin jihar ta samar domin samun sauki a maimakon su shiga irin wannan halin da bai dace ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Oresanya ya bayyana cewa jihar ta umarci dukkanin gidajen man fetur da gidajen abinci a jihar dasu samar da abubuwan jin dadin su da gidajen bahaya don amfanin jama’a a matsayin wani bangare na ayyukansu na zamantakewa.