By Abbas Yakubu Yaura
Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta ce an yankewa wani shugaban kungiyar Neo-Nazi hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari a ranar Talata bisa samunsa da yin barazana ga ‘yan jarida da masu fafutukar yaki da kyamar Yahudawa.
Kaleb Cole, mai shekaru 25, shugaban kungiyar Neo-Nazi ta Atomwaffen Division, an yanke masa hukunci a jihar Washington da ke yammacin Amurka bisa laifin aika wasiku na barazana ta hanyar sadarwa, da yin amfani da yanar gizo da dai sauransu.
An kama Cole da wasu ‘yan Nazi uku ne a farkon shekarar 2020 a wani samame da aka yi wa kungiyar a fadin kasar. Sauran mambobin Atomwaffen guda uku sun amsa laifinsu kuma an yanke musu hukunci.
A cewar masu gabatar da kara, Cole da sauran mambobin Atomwaffen sun yi yunkurin tursasawa ‘yan jarida Yahudawa da ‘yan jarida kala-kala ta hanyar aika fosta na barazana zuwa gidajensu.
Wani fosta da Cole ya ƙirƙira ya ce: “Yan Nazi na yankinku ne suka ziyarce ku.
“Wanda ake tuhumar ya jagoranci wani shiri na kasa da kasa da wata kungiyar neo-Nazi ta yi don yin barazana da kuma tsoratar da ‘yan jarida da masu fafutuka da ke yin muhimmin aiki don fallasa kyamar Yahudawa a fadin kasar.”
Lauyan Amurka Nick Brown ya ce Cole “ya ci gaba da inganta tashin hankali, tara makamai da kuma shirya ‘sansanin kiyayya.”AFP