• Hukuncin zaman gidan kaso na shekara 22 ya wajaba ga Wanda ya kashe George Floyd.
• Tsananin azabarr da Floyd ya Shane dai tayi sanadiyar mutuwar shi a hannun jami’in dan sandan.
• An yanke hukuncin ne domin jajantawa iyalan Floyd inji Mai shari’an.
An yanke wa jami’in dan sanda nan Dan wato Darek Chauvin wanda ya kashe George Floyd, hukuncin zaman gidan yarin na shekara 22.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2020 ne, jami’in dan sandan ya kama Marigayi Floyd da zargin harkallar taba sigar.
Floyd dai ya mutu ne, bisa irin tsana-nin azabar da ya sha a hannun jami’in dan sandan da ya kama shi.
Mutuwar bakin fatar, mai shekara 46, ya kawo ce-ce ku-ce a fadin duniya, wanda yasa masu zanga-zanga yin tattaki da karya dokar cutar Korona, da kuma yin dandazo a wurare daban-daban na kasar Amurika.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe matar tsohon kwamishi Nan jihar Oyo
Kazalika zanga-zangar ta yadu zuwa wasu kasashen duniya daban-daban.
A lokacin da ya ke yanke hukunci kan lamarin, Mai shari’an Kotun na Minnesota Peter Cahill ya ce” Ba wai an yanke hukuncin bane don biyan diyya, sai don jajantawa bacin ran da iyalan Floyd suka shiga, sanadiyar lamarin” inji shi.
Inda mai shari’an ya ce, “Bayanai na zasu kasanshe a ta kaica ne a nan, inda mafi ya waicin su za su zo ne a rubuce.” Kamar yadda ya ce.
Comments 1