An yanke ma wani Matashi shekara biyu gidan Kaso
Wani Matashi da ake kira James Dada Nicup dan asalin garin Makurdi babban birnin Jahar Benue, Kotu ta yanke masa hukuncin shekara biyu zaman gidan gyaran hali bayan ta kamashi da laifin damfara a yanar gizo.
Kotu ta tabbatar da kama James so biyu kenan kan laifin damfarar mutane a Facebook da WhatsApp.
KARANTA:- Shinkafi ya Gargadi Gwamna El-Rufa’i kan shiga siyasar Zamfara
Jami’an hukumar EFCC sunyi nasarar cafke James sannan suka gabatar da shi a gaban babban mai shari’a Audu Dogo a babban Kotu dake Makurdi a Jahar Benue.
In da Kotun tace ” an taba kama James a watan Satumba na shekarar 2020 yana anfani da na’ura mai kwakwalwa wajan tura ma mutane sako, da su saka kudi zai ninka musu zuwa wani lokaci, in da yayi nasarar damfarar wani da ake kira Ademu Alexandra kimanin kudi N111,900.
Bayan tabbatar da laifin sa, Kotun dai ta yanke masa hukuncin shekara biyu a gidan gyaran hali tare da biyan dubu hamsin.
In da Alkalai masu bashi kariya suka ce “muna rokon Kotu da ta yima sassauci tun da yayi ladama akan lafin sa.
Comments 1