Hukumar kula da hasken wutar lantarki a Kaduna ta yanke wutar gidan tsohon shugaban kasar Nijeriya, Marigayi Shehu Shagari saboda bashin wuta da ake bin gidan.
Rahotanni sun nuna cewa ana bin gidan Marigayin wanda ke Sama Road kusan Naira miliyan shida.
Shagari dai ya rasu a ranar 28 ga watan Disamba 2018. Ya rasu yana da shekara 93.