Tun a makon farko da aka fara sabuwar kakar wasan gasar Serea A ta ƙasar Italiya wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, an sami ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta A.S Roma da gagarumin laifi inda har aka yankemata ɗanyen hukunci wato aka zabgemata maki uku rigis a sabuwar kakar wasan ta bana, kuma hukuncin ya tabbata tun bayan da aka gano cewar ta tafka kuskuren.
Tun a ranar Juma’a 19 ga watannan na Satumba da ake ciki na shekarar 2020 aka buɗe sabuwar kakar wasan inda a waccan ranar ce ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Roma ta fafata wasanta inda ta ziyarci ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Hellas Verona kuma suka tashi kunnen doki a wasan wato abin da ake kira da kurman duro wato 0 – 0.
A waccan rana ta 19 ga watan na Satumba wasanni guda biyu aka fafata inda itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Florentina ta lashe Torino daci 1 mai ban haushi inda kuma a kaci gaba da buga sauran wasannin a ranar Lahadi yayin da Parma tayi rashin nasara a hannun Napoli daci 2 da nema, haka Genoa ta ragargaza Crotone daci 4 da 1 yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sossoulo ta buga kunnen doki wato 1 da 1 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Cagliari. Itama Juventu batayi ƙasa a gwiwa ba wajen yiwa Sampadoria wankan jego da ci 3 da nema.
A ranar Litinin kuwa A.C Milan ce ta saukewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bologna ƙwallaye guda biyu a zare inda a ranar iyaka wasan A.C Milan aka fafata kawai, sannan za a fafata ragowar sauran wasanni guda uku a ranar Laraba wato 30 ga watan Satumba inda Benevento zata fafata da Inter Milan sai kuma Udnessi da Spezia sannan kuma za a fafata wasa mafi zafi tsakanin Atalanta da Lazio.
Hukumar ladabtarwa ta gasar Serea A dai ta bayyana cewar hukuncin ƙwatar maki uku a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma ya tabbata bisa kamasu da karya doka wato yin amfani da ɗan wasan da bashi da rijista kenan, a wasan da Roma ta buga dai tayi amfani da ɗan wasan ƙasar Guinea wato Amadu Diawara inda hakan ya saɓawa dokar ta gasar Serea A.
A yanzu dak ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma tana da mami 1 tilo inda za a iya cewa ana binta bashin maki biyu kenan a nan gaba kuma tilas ta biya makin, idan za a iya tunawa a shekarun baya an dakatar da wasu manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a ƙasar ta Italiya sakamakon kamasu da a kayi da laifin sayen wasanni wato ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta A.C Milan da kuma Juventus.
Idan za a iya tunawa iya Juventus har gasar Serea B aka mayar da ita sannan kuma aka ƙwace wasu kofuna data lashe na gasar Serea A aka baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan ganin cewar lokacin da suka tafka laifuffukan ita da A.C Milan Inter Milan ce take biyemusu a baya a teburin gasar ta Serea A.