A jiya ne wata babbar kotu a Legas da ke Ikeja ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani dan sanda da aka kora, Olalekan Ogunyemi, bisa laifin kashe wani mai sha’awar kwallon kafa, Kolade Johnson.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ogunyemi, wanda ke aiki da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musamman da ke yaki da yan kungiyar Asiri, ya harbe Johnson a kasan cikinsa a ranar 31 ga Maris, 2019 a wani wurin kallo da ke yankin Mangoro, na garin Ikeja a Legas. Wanda aka kashe din yana kallon wasan kwallon kafa tsakanin Liverpool da Tottenham Hotspur lokacin da mai laifin ya harbe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kula Da Ayyukan Yan sanda Ta Yi Martani Kan Cin zarafin Teju Moses
Yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Adenike Coker ya samu wanda ake tuhuma da laifin da ake tuhumar sa da haka kuma ya yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.
Tun da farko dai ana tuhumar Olalekan da laifin kisan kai, amma kotu ta same shi da laifin kisan da ganganci.
A yayin shari’ar, mai gabatar da kara ya bada shaidu bakwai yayin da mai kare wanda ake tuhuma ya bada shaidu biyu.
A yayin shari’a, wani likitan dabbobi, Dokta Oluwaseun Williams, ya shaida cewa kotu cewa, Johnson, mai shekaru 35, ya samu raunuka harsashi shida kafin mutuwarsa.
A WANI LABARIN KUMA: Jihar Kano Na Buƙatar Ruwan Sha Lita Miliyan 200 A Kullum – Inji Kwamishinan Ruwa
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta samar da ruwan sha da ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
Malam Garba Yusuf, Kwamishinan Albarkatun Ruwa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai, a ranar Juma’a a Kano.